SAMOSA
SAMOSA Kayan hadi:- •Filawa •Butter •Gishiri •Mai •Nikakken nama •Albasa •Koran tattasai •White pepper •Thyme •Curry YADDA AKE HADAWA kwaba filawa da mai ko butter,gishiri da ruwa kamar na meat pie. rufe ajiye har zuwa minti 20. raba filawa gida 4. murza vari daya kan katakwan yanke yanke (Chopping board) har sai tayi lafai-lafai. kada yayi kauri sai a shafa man gyada akai da burushi irin na masu fenti dan karami (Pastry brush). sake dauko wani varin na filawa murza shi kamar yadda aka yiwa na farko.dura shi saman wancan da kika shafawa mai kuma murzawa.itama shafa mata mai.haka za ki tayi har agama gaba daya (ana shafa mai dan kada su manne da jikin su). idan anzo na karshe sai asa filawa. shafa mai a cikin tire irin wanda ake dora cake aciki. dauki kwabin a hankali daura kan tiren. kunna oven ki matsa kaicin zafi (moderate) har zuwa minti 20. Ko kuma idan anga ya fara dagowa yana rabuwa da junansa. fito dashi sai a yanka gida biyu dai dai. sai a nadeshi kamar kwakkwaro zuba ...