PEPPERED CHICKEN


Kaji

Maggi

Gishiri

Albasa

Curry

Citta

Taruhu

Mai

Thyme



 Da farko zaki wanke naman kajin ki bayan kin yanka su parts, saiki tsane su ki dauko tukunyan ki kijuye su, zaki sa duk kayan dandanon ki maggi curry citta thyme gishiri ki yanka albasa saiki saka ruwa daidai yadda  naman zai shanye.

Zaki bar naman ya tafasa sama sama kar yayi laushi dayawa, in ya tafasa zaku sauqe ki barshi ya tsane, saiki dauko tray kijera naman a kai kisa a oven ya gasu kamar minti goma.


Sannan zaki markada attaruhunki da albasa ya markadu kamar zakiy miya dashi, sannan saiki dorashi awuta ruwan ya qone kisoya taruhun yasoyu ki kawo dandano ki zuba da karin kayan qamshi, saiki kawo naman da kika gasa kijuye cikin kayan miyan kina juyawa a hankali har ya soyu.

Comments

Asmau Abubakar said…
Mungode
Ruky said…
Dadi kan dadi, mungode aysher

Popular posts from this blog

SNACKS

SIRRIN GIRKI