SNACKS

SAVOURY SNACKS:





CONTENT:
potato balls
Yam balls
Meat balls
Flour balls
Plantain balls
Chicken balls
Rice balls
Indian balls
Spring rolls
Fish rolls
Meat rolls
Cabbage rolls
Sausage rolls
Casse role

POTATO BALLS:
kayan hadi:
Dankali10
Nikakken nama
Albasa 1
Attarugu 2
Kwai 2
Tafarnuwa
Curry
Maggi
Gishiri
Yadda ake yi:
A tafasa dankali a bubbuga shi yayi laushi tubus. Sai a yanka albasa da attarugu a ciki. A zuba nikakken nama da maggi da gishiri da curry da tafarnuwa (idan ana bukatarta) a cakuda a hankali sai a dundunkula kamar kwallo (dai-dai girman da ake bukata.)
A fasa kwai a kada, sai a rika tsoma cure-curen dankalin a ciki sannan a soya a ruwan mai.

YAM BALLS:
Kayan yadi:
Doya 1
Nikakken nama
Kwai 4
Albasa 4
Attarugu 4
Mai
Maggi
Gishiri
Curry
Yadda ake yi :
A dafa doya sannan a bubbuga ta tayi laushi sai a hada ta da nikakken nama, a yanka albasa da attarugu, a zuba maggi, curry da gishiri. A motsa sosai sannan a rika curawa kamar kwallo, sai a tsoma a cikin ruwan kwai sannan a soya a mai.
Idan ana bukata, ana iya saka kifi a maimakon nama.

MEAT BALLS
Kayan hadi:
Nikakken nama
Albasa
Attarugu
Kwai
Mai
Tafarnuwa
Garin busasshen buredi yadda ake yi :
A hada nikakken nama ko dakakken nama da yankarkiyar albasa a kuma yanka attarugu, tafarnuwa, maggi, gishiri, a cakuda sosai. Sai a fasa kwai daya a ciki, a sake cakudawa sai a cura kamar kwallo a saka a ruwan kwai, sannan a barbade da garin busasshen burodi sai a soya a mai.

FLOUR BALLS
kayan hadi:
Filawa kofi 2
Kifin gwangwani 1
Albasa1
Attarugu 2
Yeast karamin cokali 1
Mai
Kayan kanshi
Gishiri
Maggi
Yadda ake yi :
A zuba yeast cikin ruwan dumi, sannan a hankali a rika zuba filawa ana motsawa, sai a rufe a sa a rana kamar awa 4.
Idan ta kumbura sosai, sai a zuba kifi gwangwani 1, a yanka albasa da attarugu, a zuba maggi, gishiri da kayan kanshi a motsa sosai, sai a rika zubawa a cikin ruwan mai ana soyawa, ana iya zubawa da cokali ko da hannu yadda dai zai zama kamar kwallo.

PLANTAIN BALLS
Kayan hadi:
Filawa kofi 1 da rabi
Sikari kofi 1 da kwata
Bakar hoda cokali biyu
Madara kofi daya da rabi
Kwai 1
Plaintain nunanne 1
Mai
Yadda ake yi:
A bare a yan-yanka plantain kanana, a hada da kwai da sikari, da filawa, da bakar hoda da madara, a juya a hankali su hadu, kada a kada. Sai a rika diba da cokali ana soyawa a ruwan mai. Idan bari daya ya soyu, sai a juya daya barin.

CHICKEN BALLS
Kayan hadi :
Kaza1
Dankali 1
Albasa 2
Tumatur 1
Tattasai 1
Attarugu 2
Kwai 2
Mai
Maggi
Gishiri
Curry
Yadda ake yi:
A tafasa kaza, a cire kashin a zuba tsokar a kwano, a hada da dakakken dankali(tafasasshe) a yanka albasa, tumatur, attarugu da tattasai a hada da maggi, gishiri da kayan kanshi duk a motsa tare da kwai, sai a cuccura a soya a ruwan mai.

RICE BALLS
Kayan hadi:
Shinkafa
Nama
Kwai
Kayan miya
KO
shinkafa
Sikari
Kwa- kwa
Kwai
Yadda ake yi:
A tafasa shinkafa da ruwa ta dahu sosai, a bari ta huce sai a juye a babban kwano, a fasa kwai a zuba a motsa, idan tayi ruwa-ruwa, sai a zuba filawa kadan domin yayi kauri, a yanka kayan miya kadan a zuba maggi da gishiri a cuccura a soya a ruwan mai.
Idan kuma mai zaki ake so, sai a zubawa shinkafa sikari da kwakwa (gurzarza) a cuccura a soya a mai.

INDIAN BALLS
Kayan hadi:
Dankali 10
Nama
Na'a-na'a
Garin biredi
Mai
Albasa 1
Tattasai 1
Attarugu 1
Gishiri
Maggi
Kayan kanshi
Yadda ake yi :
A hada tafasasshen nama da tafasasshen dankali a markada a blender, a zuba na'a-na'a, maggi, gishiri da kayan kanshi, a kuma yanka kayan miya a hada su sosai sai a rika dunkulawa ana sawa a cikin garin biredi kafin a soya a ruwan mai.

SPRING ROOLS
Kayan hadi :
Kabeji 1/6
Karas 2
Albasa 1
Filawa kofi 2
Kwai 2
Nikakken nama
Mai
Maggi
Gishiri
Curry
Buroshi( irin na cikin kayan girki)
Yadda ake yi:
A yanyanka kabeji da albasa da karas a soya sama-sama tare da mai cokali daya, a zuba nikakken ko dakakken nama, maggi, gishiri da curry sai a sauke daga kan wuta.
A hada filawa, kwai, maggi, gishiri da ruwa a kwaba,yayi kamar kaurin koko. A shafa mai a ciki [truncated by WhatsApp]

Comments

Popular posts from this blog

SIRRIN GIRKI