ADO DA KWALLIYA
Jama'a barkanmu da dare.
Acikin filinmu na ado da kwalliya yau
zamu fadi yadda ake gyara fuska da
yadda akewa fuska kwalliya,saboda
fuska tanada makuqar muhimmanci
da jan hankali acikin kwalliya.
Zamu fara da yadda ake gyara fuska
kafin ayi mata kwalliya,yadda fuska
zatai taushi da haske sannan bazatai
kurajeba ,tayadda bazamu kashe
kudinmu wajen siyan man qara
hasken fuska ba wato(lightening
cream).
masu kurajen fuska zasu samu
lemon tsami a matseshi a hada
ruwansa da ruwan veniger wato(ma'u
khal)saiki shafa da auduga a hankali
kibarshi yai minti 20(akiyaye karya
shiga ido).
Ana kwaba lalle da sai asa dan
ruwan ma'u khal acikinsa sai a shafa
a fuska a barshi yai minti 10,yanasa
taushi da hasken fata,fatarki zatayi
danja maiban sha'awa.
'bawon Gwanda yana maganin
kurajen fuska kuma fuska zatai santsi
za a gogashi a fuska sai a barta tayi
minti 30 kafin a wanke.
'Bawon kankana da tumatur yana
gyara fuska shima za a gogashi
abarshi yai minti 20 sai a wanke.
kurkum da kwai inkika hadasu saiki
shafa a fuska yau minti 20 saiki goge
da man zaitun kafin ki wanke.
Masu bakar fata zasu sami nescafe da
dan ruwa kadan a shafe fuska
dashi,idan yasha iska sai a ringa
daukewa da hannu amma Masu
sensitive skin idan sunyi suyi saurin
shafa lemon tsami,saboda kar kuraje
su fito a fuskar wannan hadin yana da
kyau yana dauke gashin fuska basai
kinyi halawaba.(amaso ki dinga
wanke fuskar da ruwan dumi).
Toh bayan kin dauki wanda zakiyi
acikin su,anaso kafin kishifa mai
kisamu baby wiper mai aloevera
kidinga gogawa a fuska yadda dinshin
wiper din zaishiga cikin fatar,tanasa
fata tayi taushi da santsi Kamar
auduga sannan tana dauke da
abubuwa Masu amfani ga fuska.
Toh bayannan saiki shafa man ridi
(wato man kantu)amfaninsa yana
gyara fata yana kashe kuraje sannan
duk wani tamoji tamojin fuska zai
bace,inkuma kinada man dayakarbeki
saiki shafa a kula da cika mai a fuska
a dinga shafa dan kadan.
Bayan kinshafa manki saiki samu
foundation dinki ki tatsi dai dai misali
karki cikata saiki shafa,ki tabbatar ko
ina yasamu amfaninta tana dauke
gumin fuska tana haskaka fuska tayi
kyau sosai da sosai.
Yanzu kuma sai shafa hoda,Toh itama
powder kala - kala ce kowace kalar
fata akwai hodar da yakamata a shafa
mata,akwai kuma wadda zataiwa fara
da bakar fata kyau itace farar hoda,sai
jar hoda wato(cake powder) akwai ta
farare akwai kuma ta bakake .
Jar powder mai haskenta itace ta
Masu bakar fata.
Jar powder mai duhu itace ta Masu
farar fata.
Toh kowace mace saita dubi kalar da
Allah yaimata,saita dauki wadda zata
dace da ita saboda kwalliyarta tai yau
da tsari yadda in aka kalleki za aga
kamar shekarunki basukai nakiba.
Wasu matan kanyi kuskure wajen
yadda zasu shafa hoda,don Hakane
mukayimaku guzirin bayani dan
kaucewa kura kurai yayin
shafata,wasu matan kan fara shafa
hoda daga kumatu Wanda hakan
kansa asami bambancin yawan hodar
a fuska, Wanda hakan kansanya
asami yawan goge goge a fuska,
inzaki shafa hoda anaso a fara daga
goshi sannan a taho zuwa
haba ,bayan haka anaso a dinga
amfani da faffadan soso wajen shafa
hoda yana rage yawan dabbare-
dabbare da za a rika samu.
Toh 'yan uwa anan zamu dakata sai
wani makwan insha Allah zamu kawo
maku ci gaba na wani nau'in na
kwalliya.
Acikin filinmu na ado da kwalliya yau
zamu fadi yadda ake gyara fuska da
yadda akewa fuska kwalliya,saboda
fuska tanada makuqar muhimmanci
da jan hankali acikin kwalliya.
Zamu fara da yadda ake gyara fuska
kafin ayi mata kwalliya,yadda fuska
zatai taushi da haske sannan bazatai
kurajeba ,tayadda bazamu kashe
kudinmu wajen siyan man qara
hasken fuska ba wato(lightening
cream).
masu kurajen fuska zasu samu
lemon tsami a matseshi a hada
ruwansa da ruwan veniger wato(ma'u
khal)saiki shafa da auduga a hankali
kibarshi yai minti 20(akiyaye karya
shiga ido).
Ana kwaba lalle da sai asa dan
ruwan ma'u khal acikinsa sai a shafa
a fuska a barshi yai minti 10,yanasa
taushi da hasken fata,fatarki zatayi
danja maiban sha'awa.
'bawon Gwanda yana maganin
kurajen fuska kuma fuska zatai santsi
za a gogashi a fuska sai a barta tayi
minti 30 kafin a wanke.
'Bawon kankana da tumatur yana
gyara fuska shima za a gogashi
abarshi yai minti 20 sai a wanke.
kurkum da kwai inkika hadasu saiki
shafa a fuska yau minti 20 saiki goge
da man zaitun kafin ki wanke.
Masu bakar fata zasu sami nescafe da
dan ruwa kadan a shafe fuska
dashi,idan yasha iska sai a ringa
daukewa da hannu amma Masu
sensitive skin idan sunyi suyi saurin
shafa lemon tsami,saboda kar kuraje
su fito a fuskar wannan hadin yana da
kyau yana dauke gashin fuska basai
kinyi halawaba.(amaso ki dinga
wanke fuskar da ruwan dumi).
Toh bayan kin dauki wanda zakiyi
acikin su,anaso kafin kishifa mai
kisamu baby wiper mai aloevera
kidinga gogawa a fuska yadda dinshin
wiper din zaishiga cikin fatar,tanasa
fata tayi taushi da santsi Kamar
auduga sannan tana dauke da
abubuwa Masu amfani ga fuska.
Toh bayannan saiki shafa man ridi
(wato man kantu)amfaninsa yana
gyara fata yana kashe kuraje sannan
duk wani tamoji tamojin fuska zai
bace,inkuma kinada man dayakarbeki
saiki shafa a kula da cika mai a fuska
a dinga shafa dan kadan.
Bayan kinshafa manki saiki samu
foundation dinki ki tatsi dai dai misali
karki cikata saiki shafa,ki tabbatar ko
ina yasamu amfaninta tana dauke
gumin fuska tana haskaka fuska tayi
kyau sosai da sosai.
Yanzu kuma sai shafa hoda,Toh itama
powder kala - kala ce kowace kalar
fata akwai hodar da yakamata a shafa
mata,akwai kuma wadda zataiwa fara
da bakar fata kyau itace farar hoda,sai
jar hoda wato(cake powder) akwai ta
farare akwai kuma ta bakake .
Jar powder mai haskenta itace ta
Masu bakar fata.
Jar powder mai duhu itace ta Masu
farar fata.
Toh kowace mace saita dubi kalar da
Allah yaimata,saita dauki wadda zata
dace da ita saboda kwalliyarta tai yau
da tsari yadda in aka kalleki za aga
kamar shekarunki basukai nakiba.
Wasu matan kanyi kuskure wajen
yadda zasu shafa hoda,don Hakane
mukayimaku guzirin bayani dan
kaucewa kura kurai yayin
shafata,wasu matan kan fara shafa
hoda daga kumatu Wanda hakan
kansa asami bambancin yawan hodar
a fuska, Wanda hakan kansanya
asami yawan goge goge a fuska,
inzaki shafa hoda anaso a fara daga
goshi sannan a taho zuwa
haba ,bayan haka anaso a dinga
amfani da faffadan soso wajen shafa
hoda yana rage yawan dabbare-
dabbare da za a rika samu.
Toh 'yan uwa anan zamu dakata sai
wani makwan insha Allah zamu kawo
maku ci gaba na wani nau'in na
kwalliya.
Comments
nima nagode