FARFESUN KIFI


kifi
Citta
Taruhu
Kanin fari
Curry
Thyme
Albasa
Maggi
Tafarnuwa
Gishiri
Daddawa inkina so


 Da farko zaki wanke danyen kifinki da lemon tsami don ya rage qarni ki wanke kifin sosai,  saiki jerashi yasha iska, sannan zaki dauko taruhun ki ki jajjaga shi, saiki daka citta kanimfari ya zama gari, sannan in zakisa daddawa ita ma ki dakata ta zama gari, in bakya buqata shikenan, zaki yanka albasan ki yanka manya manya, sannan saiki dora ruwa daidai yadda bazai rufe kifin ba a tukunya ya tafasa, zaki kawo kayan miyanki taruhu, daddawa, kanimfarin citta, maggi gishiri  ki juye a ruwan yayi ta tafasa sai warin daddawan ya fita saiki kawo kifin ki kijera a tukunyan, ki kawo albasan ki kijuye da curry da thyme, ki dan gurza tafarnuwa kadan,  sai ki rufe tukunyan ki lura kifi bashida wahalan dahuwa in ya dahu da yawa zai farfashe, aci dadi lafiya # ayyush

Comments

Salma adam said…
Yayi
Laurat usman said…
Yummy

Popular posts from this blog

SNACKS

SIRRIN GIRKI