FRIED RICE



-shinkapa

-naman kaza

-mai

-butter

- knoor chicken

-gishiri

-curry

-thyme

-albasa

-karas

-peas

-koren wake

-hanta

-koren tattasai


  Da farko uwargida zaki wanke naman kajin ki tas, saiki zubashi tukunya ki yanka masa ishashshen albasa ki kawo curry, thyme, knoor chicken, gishiri, saikisa ruwa kudora naman awuta ya tafasa har qarnin ya fice karki bar naman ya dahu sosai, saiki sauqe kijuye naman ki soya shi, kibar ruwan tafasan naman kajin a tukunyan ki.


  Zaki dauko wannan ruwan tafasan naman kajin da kika aje ki dora awuta ki qara masa kayan dandanon ki knoor chicken, curry thyme gishiri daidai dandanon ki, sannan saiki wanke shinkafanki daidai wadda kike buqata kibar ruwan tafasan kajin ya tafasa saiki kawo shinkapan ki ki juye, daga nan zaki barshi ya tafasa amma kar shinkapan yayi laushi sosai da zaran ruwan ya tsotse saiki sauqe ta.

  Zaki dauko vegetables dinki ki wanke su, karas ki kankare shi sosai sannan saiki yanka shi irin shape din da kikeso round ko cube zaki yanka koren tattasan ki ma qanana ki hadasu da koren waken ki da peas, saiki kawo butter ki zuba a fryn pan/abin suya kibarshi yafara zafi saiki juye karas waken peas da koren tattasan ki kina juyawa a hankali har suyi laushi ba sosai ba, saiki juye su,

  Zaki yanka hanta qanana kisa albasa kikawo kayan qamshi ki zuba da kayan dandano kibarta tadan tafasa ba sosai ba saiki soyata sama sama ki juye.


 Yanzu zaki samu fryn pan dinki saiki hada butter da man girki kizuba kadan kadan kidebo shinkapan ki dakika dapa ki zuba, ki debo hanta ki zuba, ki debo su karas dinki ki zuba saiki na juyasu suna soyuwa a hankali wuta kadan, har ya soyu saiki juye ki qara debo shinkapan ki kina hadawa da sauran kayan hadin haka har kigama aci dadi lafia. #ayyush

Comments

nusaiba bala said…
Tnx alot
Samira abdul said…
Godiya muke sis
Samira abdul said…
Godiya muke sis
😊😋😋 said…
Good
Safiya ahmad said…
Kai sis kina qoqari Allah ya saka da alkhairi

Popular posts from this blog

SNACKS

SIRRIN GIRKI