DAMBUN NAMA



  Yadda zakiy danbu mai laushi da dadi kuma baya lalacewa koda zai dade.


Nama
Maggi
Curry
Thyme
Gishiri
Tafarnuwa
Citta
Albasa
Taruhu

 Da farko zaki zabi  wajen nama mara kitse kuma maras jijiya tsoka zalla akeso sai an yanka miki manya manya basai anyi yanka qanana ba, sannan in a lokacin akayi yanka namanki ba datti basai kin wanke ba, kawai zaki samo tukunya mai dama ki juye naman ki.

Saiki kawo kayan hadinki ki zuba gishiri kisa kadan, maggi tafarnuwa a daka ta, albasa, thyme, citta adaka ta, albasa, curry duk ki juye saiki mixn naman sosai saiki barshi zuwa 1 hour,

 Daga nan zaki dauki tukunyan naman ki kidora wuta ki zuba ruwa kwatankwancin yadda zai shanye naman yagama laushi yadda dakin taba naman da muciya  zakiga ya fashe to ya gama laushi,


Zaki sa muciyan ki kina tuqawa kina fasa naman har sai gaba daya ya fashe yayi sanka sanka.

Sannan akwai zabi biyu zaki iya suyan tukunya ko abun suya nama, idan na tukunya ne zaki dauko mai na suya ko na gyada ko na kanti, kisa albasa ki soya shi  kijuye kan naman ki ki jajjaga taruhun ki kisa saiki fara tuqashi da muciya amma kisa wuta kadan a hankali kina tuqawa har sai kinga mai yafara kumfa to ya soyu,

Idan suyan abun suya ne ma haka zaki yi ki soya manki da albasa ki kawo naman ki juye ki jajjaga taruhun ki ki juye zaki iya qara abin da baiji ba curry ko citta, saiki sa mara kina juyawa akai akai kuma a wuta kadan karki barshi ya kama sbd bazai dadi ba in yayi qauri,  sannan inda yawa yana daukan lokaci saikin daure baa sa wuta sosai, daya soyu saiki samu colander  kisa kwano a qasa ki juye ki dora plate asama kina dannawa har sai mai ya fita saiki barshi ya huce saiki juye shikenan, #AYYUSH

Comments

Popular posts from this blog

SNACKS

SIRRIN GIRKI