🍲```GIRKE-GIRKE```🍛 _YADDA AKE HADA *ICE CREAM* Vanilla🍦 da Chocolate🍧_ *ABUBUWAN DA AKE BUKATA* 1⃣Ruwan kwai (farin kawai) 2⃣Madara ta ruwa ko ta gari 3⃣Vanilla Flavour 4⃣Pure cocoa 5⃣Maltisers chocolate 6⃣Sukari 'Icing' na yin cake _*YADDA AKE HADAWA*_ _HADIN VANILLA_:🍦 _Da farko sai a fasa kwai kamar biyar sannan a tsane gunduwar (kwaiduwar) da ke cikinta sai a zuba a blender. Bayan haka, sai a zuba madara da sukari na yin *cake* (Icing sugar). Sannan sai a diga flavour na vanilla a ciki sannan sai a markada su har sai sun yi kumfa sai a zuba a roba sannan a sanya shi a gidan sanyi (fridge) ya yi kankara._ _HADIN CHOCOLATE_:🍧 _A zuba madara da sukarin yin *cake* a na'urar markade ta gida (blender). Sannan a dauko cokali daya na 'pure cocoa' a zuba sannan a zuba *flavour* na kwakwa._ _Sannan sai a markada har sai ya yi kumfa sannan a zuba a roba. A dauko *chocolate* na maltisers a jefa a cikin hadin sannan a saka a gidan sanyi ...
Posts
Showing posts from 2016
SAMOSA
- Get link
- X
- Other Apps

SAMOSA Kayan hadi:- •Filawa •Butter •Gishiri •Mai •Nikakken nama •Albasa •Koran tattasai •White pepper •Thyme •Curry YADDA AKE HADAWA kwaba filawa da mai ko butter,gishiri da ruwa kamar na meat pie. rufe ajiye har zuwa minti 20. raba filawa gida 4. murza vari daya kan katakwan yanke yanke (Chopping board) har sai tayi lafai-lafai. kada yayi kauri sai a shafa man gyada akai da burushi irin na masu fenti dan karami (Pastry brush). sake dauko wani varin na filawa murza shi kamar yadda aka yiwa na farko.dura shi saman wancan da kika shafawa mai kuma murzawa.itama shafa mata mai.haka za ki tayi har agama gaba daya (ana shafa mai dan kada su manne da jikin su). idan anzo na karshe sai asa filawa. shafa mai a cikin tire irin wanda ake dora cake aciki. dauki kwabin a hankali daura kan tiren. kunna oven ki matsa kaicin zafi (moderate) har zuwa minti 20. Ko kuma idan anga ya fara dagowa yana rabuwa da junansa. fito dashi sai a yanka gida biyu dai dai. sai a nadeshi kamar kwakkwaro zuba ...
FANKE
- Get link
- X
- Other Apps

Abin Bukata filawa kofi 2 kofi 1 1/2 na ruwan dumi ckb 1 na yis 1/2 na sikari kc 1 na gishiri vanilla don dandano albasa kankararriya yadda za ayi a zuba yis cikin ruwan dumi don ya narke sai a zuba akan filawa tare da sikari, gishiri da vanilla a kwaba su baki daya yayi dan tauri a sami wuri me dumi a ajiye don ya tashi a sami kamar awa daya. a dora mai a wuta idan yayi zafi sai kisa hannunki ki dinga yankowa kina sawa a cikin man. idan ya soyu zaki ga ya zama ruwan kasa. za a iya ci da shayi ko kunu ko lemo. kada amanta kwabin kada ya zama ruwa-ruwa ko yayi tauri. aci dadi lafiya
SARRAFA KWAI
- Get link
- X
- Other Apps
SARRAFA KWAI CI KAYI SANTI Ingredients: * Kwai * Nama * Curry * Maggi * Gishiri * Tumatir Procedures: Ki dafa kwanki, daidai yawan da kike so ki yanka shi kanana, ki yanka tumatir, attarugu da albasa akai ki yanka tafasasshen namanki kanana a kai, ki fasa kwan ki zuba akai, kisa maggi, curry, gishiri, ki kada ya kadu sosai, ki dora mai a kan wuta ki soya kamar suyar wainar kwai. SUYAR KWAI MAI NAMA Ingredients: * kwai * Nama * Maggi da gishiri * Curry * Albasa * Attarugu Procedures: Ki tafasa namanki da maggi, curry, thyme, albasa, ki daka shi sosai, ki fasa kwai ki yanka albasa, attarugu, ki zuba dakakken nama, ki karo maggi da gishiri daidai yadda kike so, ki kada sosai, ki soya kamar wainar kwai. NAMA CIKIN KWAI Ingredients: * Kwai * Nama * Gishiri da Maggi * Albasa * Attarugu * Mai Procedures: Ki dafa kwanki daidai yawan da kikeso, kowanne ki yanke kasansa wajen fadin kadan ki kwakule kwanduwar a hankali ki cire ta, ki tafasa namanki da curry, thyme, maggi, gishiri. Idan ya dahu ki...
COCONUT RICE
- Get link
- X
- Other Apps
Abin Bukata ruwan kwakwa kofi 5 shinkafa gwangwani 3 timatir manya 5 timatirin gwangwani 1 mai madaidaici kanunfari kc1 gishiri don dandano ganye bay kadan albasa attaruhu kadan tafarnuwa Yadda Za Ayi a dafa ruwan dumi a zubawa shinkafa kafin a dafa ta. a jajjaga attaruhu tare da tafarnuwa. asa mai a wuta idan ya soyu sai a zuba jajjagaggun kayan miya a kawo timatirin gwangwanin nan a zuba akai su soyu gaba daya idan sun soyu sai a zuba ruwan kwakwan nan akai tare da ganyen bay. daya tafaso sai a wanke shinkafa a zuba a rufe ta idan ana so a hada ta dankalin turawa a zuba mata gishiri daidai gwargwadon bukata. idan ta dahu za a iya cin ta da naman kaza soyayyaye ko kifi. wannan dafadukar wata nauin dafaduka ce da babbain ta da wanda aka sani shine ruwan kwakwa da aka sa. a wasu kashen afrikan ake yinta kamar cameroun kuma ana girka ta da nama amma wannan na bada zabi za a iya anfani da abin da ake bukata.kamar wanda basa cin nama zasu iya anfani da wannan hadin.
MIYAR WAKE
- Get link
- X
- Other Apps
ABUBUWAN BUQATA WAKE MANJA BUSHASHSHEN KICI (BANDA) ALBASA MAGGI GISHI DA SAURAN KAYAN DANDANO ATTARUHU Idan uwargida ta samo wakenta saita jiqa shi idan yajiqu zata gyara shi ta cire bawon waken tsaf saita dora ruwa awuta idan ya tafasa saita kawo waken tazuba tabar shi yayi ta tafasa sai ya dahu sosai saita kawo yankakkiyar albasa da attaruhunta ta juye takawo manja soyayye da gyararren kifin ta duk ta juye sai ta jira miyar ta sake dahuwa sannan takawo kayan dandanon datake buqata maggi gishiri DSS. daga nan zata sake barinta ta dan jima a wuta kadan kadan da zaran taga miyar yayi saita sauqe zaa iyaci da tuwon shinkapa ACI DADI LAFIA #AYYUSH
SHISH KEBAB
- Get link
- X
- Other Apps
Shish kebab *Nama manya kilo 1 * albasa manya 3 *mai dandano 3 *gishiri *koren tattasai 2 *man gyada 2tin *tumatir manya 2 "Tafarnuwa 5 opt Sami namanki me kyau ki nike shi ko ki kirba a turmi, zuba yankakkiyar albasa,mai dandano,tafarnuwa,gishiri, wajen dakan ko nikan. Kwashe ki dinga mulmulashi daidai tsayi da kaurin Dan yatsa. Se ki soya a mai amman kar ya karau ko kuma ki gasa domin ya ma fi armashi. Se kiyi decorating da slices din tumatur da albasa a gefen naman gado gado.ki watsa mishi yankakken Koren tattasai kanana kanana(a cire yayan ciki),a yaryada ketchup. A ci shi da roti ko gubza
MATA A KITCHEN
- Get link
- X
- Other Apps
[4/5, 9:48 AM] Aunty Ayyush: Chicken Curry Ingredients Vegetable oil 1 cinnamon stick 2 green cardamom pods 1 Teaspoon Cumin seed 1 finely chopped, medium onion Small piece Ginger crushed 6 garlic cloves crushed 1/2 Teaspoon turmeric 1/2 Teaspoon coriander 1/2 Teaspoon Chilli powder 2 puréed tomatoes 4-5 chicken breast cut into cubes Teaspoon Garam masala Method * Start by adding oil to a large frying (about 3-4 tablespoons) pan over a medium to high heat. Add the garlic, cinnamon, cardamom and a teaspoon of cumin seeds and cook for around 30 seconds. * Add the onion and cook until soft and golden. * Stir in a table spoon of ginger and coriander, garlic, half a teaspoon of chilli and turmeric and a pinch of salt and pepper. * Add the tomatoes and cook until the liquid in the pan has dried out (around 10 minutes should do).Place the chicken in the pan and cook for around 3 minutes until browned. * Pour in around 300ml of water and allow to cook on a gentle heat for around 20 minutes. * ...
FALALAR ALWALA
- Get link
- X
- Other Apps
DARIQUS SALIHEEN ILAA RABBIL AALAMEEN NA WAHEED ABDUSSALAAM BAALIY 3 FALALAR ALWALLA ALWALLA ALAMU CE DAKE NUNA MUSULMAI RANAR QIYAMA Muslim ya ruwaito daga Abu Hurairata RA lallai Manzon Allah (saw) ya je maqabarta sai yace "ASSALAMU ALYKUM DAARA QAUMIN MU'UMININA WA INNA IN SHAA ALLAHU BIKUM LAAHIQUUN, naso ace munga enuwanmu " sai Sahabbai sukace 'ba mu bane enuwanka Ya RasulilLah' sai yace "Ku abokaina ne, enuwanmu kuwa sune wadanda ba Su zo ba sai bayan bamu", sai sukace 'to ta ya zamu gane al'ummar Ka Ya RasulilLah' sai yace "ba kwa ganin da ace dokin mutum mai haske a fuska da qafa da kuma bayan shi baqiqqirin, ashe ba zai gane dokinsa ba". Sai sukace 'eh zai ganeshi Ya RasulilLah'. Sai yace "to Su din zasu zo suna masu hasken fuska da qafafuwa don Alwalla, Ni kuma zan wuce gaba akan wani tafki, sai dai wasu zasu taho sai a koresu daga tafkina, kamar yadda ake korar bataccen Raqumi, Ni kuma ina kiransu Ku taho Ku...
QWAI CIKIN QWAI
- Get link
- X
- Other Apps
Abubuwan da za a bukata • kwai • Magi • Hanta • Kori • Albasa • Attarugu • Man gyada • Leda Hadi A samu kwai kamar guda biyar. Sai a wanke su da soso da sabulu. Sannan a kula domin kada kwan ya fashe. Idan an gama wankewa, kuma an dauraye sai a ajiye shi a gefe. A wanke hanta sannan a sulala shi da albasa ya nuna ya yi laushi sosai. Sannan a yayyanka shi kanana sosai a ajiye a gefe. A jajjaga attarugu, shi ma a ajiye a gefe. A yayyanka albasa kanana sosai a ajiye. A samu kwan nan da aka wanke a dan bantare samansu kadan ba tare da an fasa bawon ba. Sannan sai a zazzage ruwan a kwano. A zuba yankakkiyar hantar da albasar da jajjagaggen attarugu da magi sannan sai a kada su. A zuba magi da kori kadan. In ana cin tafarnuwa ma sai a dan zuba garinta kadan, sannan a sake kada kwan. Bayan haka, sai a diga man gyada kadan a cikin kwan sannan a zuba wannan ruwan kwan da aka yi wa hadin a bawon kwan a saka a leda a kulle shi, yadda ruwan kwan ba zai zuba ba. A dora ruwa a wuta. Bayan ruwan ya t...
SIRRIN GIRKI
- Get link
- X
- Other Apps
SIRRIN GIRKI, idan kinason shinkafarki tayi warawara, ki wanke da gishiri, ko kuma ki jikata acikin ruwan dumi tsawon minti 30 sannan kidafa idan kinaso shinkafar tayi haske kidansa lemun tsami idan farar shinkafa zakiyi mai carrot da peas da green beans sai kisa masu baking powder bayan kin dafasu daban zakiga kalarsu tafito kuma shinkafar tayi kyau saboda basu taba taba idan bakiso kiji yaji wajen yanka albasa kici chewing gum, a lokacin dakike yankawa idan kin kone kafin kice komai zakice kulna ya naaru bardan wassalamu ala ibrahim ko ki shafa danyen kwai ko ruwan kanwa in sha Allahu bata tashi. idan kinaso spaghetti tayi warawara saiki kashe kafin tadahu har tayi lugub saiki chanza ruwa kiyi straining a kwando zogale da alayyahu suna rage warin zufa da tsamin jiki, especially masu yawan cin tafarnuwa da danyan albasa dakin yanka albasa ko tafarnuea zakiyi sauri ki wanke hannunki da lemun tsamu saboda gudun wari idan kinaso a abincinki yayi kamshi curry, tarugu da thyme, suzama ...
vegetable sauce
- Get link
- X
- Other Apps
VEGETABLE SAUCE INGREDIENTS: 1.Fish,Oil 2.Lawashi, Tomatoes, 3.Alayyaho/Ugwu ,green beans 4.Maggi, gishiri 5.Kanunfari, citta, curry, thyme, onga da sauran kayan kamshi. PROCEDURE: Ki sami kifi mai kyau ki gyara ki wanke, ki zuba a tukunya, ki wanke tukunya ki sa a wuta, yana fara zafi sai ki dauko kifi ko nama ko kaza ki sa a ciki, sai ki sa maggi amma kada ki farfasa ki sashi a haka, sai ki dauko isashen lawashin da kika yanka, ki juye a ciki, ki dauko carrots da kika kankare kika yanka kanana ki juye a ciki, ki sa green beans daga nan sai ki dauko ruwa wanda zai shanye kan kifin ko kazan ki zuba a ciki. Ki zuba mangyada dan dai-dai, sai ki rufe ki barshi ya tauso. Daga nan sai ki jajjagaga tumatir ko ki yanka, idan kuma kina son su tarugu duk sai ki sa, ki sa gishiri, curry, thyme, citta, onga da sauran kayan kamshin da na lissafo sai ki rufe ya cigaba da dahuwa, sai ki dauko yankakken alayyahon ki zuba a sama, ki rufe, bayan kamar 5mnt sai ki dan jujjuya, a hankali zaki yi saboda k...
TARBIYYA TA MUSLUNCI
- Get link
- X
- Other Apps
السلام عليكم ورحمة الله وبركاته بسم الله الرحمن الرحيم Insha Allahu zanyi lecture mae taken. TARBIYYAH TA MUSULUNCI Tarbiyyah da gina kyawawan dabi,u sune tushen gina akida da ingancin musulunci, Mutum baya zama musulmi na gaskiya ba tare da yayi kyawawan dabi,uba. Imani da kyawawan dabi,u tare sukw daya baya samuwa ba tare da ansamu daya ba. Saboda haka musulunci ya kula da kyawawan dabi,u da halaye na gari,kulawa wadda babu irinta har Manzon Allah s.a.w yace"Ba,a aikoni don komae ba sae don in cika kyawawan dabi,u". Wannan ya nuna musulunci ba komae bane sae kyawawan dabi,u. Manzon Allah s.a.w yace" Kayi mu,amala da mutane da kyakkyawar dabi,ah". Tirmixi ya ruwaito Yanzu da yawa idan muka duba yaran mu mata da maza akwaearancin tarbiyyah. Wasu ma babu tarbiyya kwata-kwata wasu iyayen sunbar yaransu kara xube sae abnda sukagadama shi zasuyi basu iya nuna musu abu mae kyau da marar kyau. Duk abnda sukayi dae daene. Shin ko so ne yake kawo hakan ❓DAYAWA DAGA CIKIN MA...