SHISH KEBAB
Shish kebab *Nama manya kilo 1 * albasa manya 3 *mai dandano 3 *gishiri *koren tattasai 2 *man gyada 2tin *tumatir manya 2 "Tafarnuwa 5 opt Sami namanki me kyau ki nike shi ko ki kirba a turmi, zuba yankakkiyar albasa,mai dandano,tafarnuwa,gishiri, wajen dakan ko nikan. Kwashe ki dinga mulmulashi daidai tsayi da kaurin Dan yatsa. Se ki soya a mai amman kar ya karau ko kuma ki gasa domin ya ma fi armashi. Se kiyi decorating da slices din tumatur da albasa a gefen naman gado gado.ki watsa mishi yankakken Koren tattasai kanana kanana(a cire yayan ciki),a yaryada ketchup. A ci shi da roti ko gubza
Comments