FALALAR ALWALA

DARIQUS SALIHEEN ILAA RABBIL AALAMEEN NA WAHEED ABDUSSALAAM BAALIY 3 FALALAR ALWALLA ALWALLA ALAMU CE DAKE NUNA MUSULMAI RANAR QIYAMA Muslim ya ruwaito daga Abu Hurairata RA lallai Manzon Allah (saw) ya je maqabarta sai yace "ASSALAMU ALYKUM DAARA QAUMIN MU'UMININA WA INNA IN SHAA ALLAHU BIKUM LAAHIQUUN, naso ace munga enuwanmu " sai Sahabbai sukace 'ba mu bane enuwanka Ya RasulilLah' sai yace "Ku abokaina ne, enuwanmu kuwa sune wadanda ba Su zo ba sai bayan bamu", sai sukace 'to ta ya zamu gane al'ummar Ka Ya RasulilLah' sai yace "ba kwa ganin da ace dokin mutum mai haske a fuska da qafa da kuma bayan shi baqiqqirin, ashe ba zai gane dokinsa ba". Sai sukace 'eh zai ganeshi Ya RasulilLah'. Sai yace "to Su din zasu zo suna masu hasken fuska da qafafuwa don Alwalla, Ni kuma zan wuce gaba akan wani tafki, sai dai wasu zasu taho sai a koresu daga tafkina, kamar yadda ake korar bataccen Raqumi, Ni kuma ina kiransu Ku taho Ku taho, sai ace 'ai wadannan haqiqa sun canza bayanka', sai ince can dai can dai". MUSLIM (249) Muhallish shaahid a wannan hadisin shine cewar mutane zasu zo suna masu haske a guraben alwallarsu. To sai qarin bayanin wadanda za'a kora sune wadanda suka canza daga koyarwar Manzo (saw), sannan kuma ruwan tafkin da Manzon Allah (saw) zai kaimu shine tafkin alkausara wanda in an Shaa ruwanshi to ba sauran qishi kuma. Allah Ka shayar damu wannan ruwa. Aameen UMMAHATUL MUMININ 08062710092

Comments

Popular posts from this blog

SAMOSA

SNACKS