🍲```GIRKE-GIRKE```🍛

_YADDA AKE HADA *ICE CREAM* Vanilla🍦 da Chocolate🍧_





 *ABUBUWAN DA AKE BUKATA*

1⃣Ruwan kwai (farin kawai)
2⃣Madara ta ruwa ko ta gari
3⃣Vanilla Flavour
4⃣Pure cocoa
5⃣Maltisers chocolate
6⃣Sukari 'Icing' na yin cake

 _*YADDA AKE HADAWA*_

_HADIN VANILLA_:🍦
 _Da farko sai a fasa kwai kamar biyar sannan a tsane gunduwar (kwaiduwar) da ke cikinta sai a zuba a blender. Bayan haka, sai a zuba madara da sukari na yin *cake* (Icing sugar). Sannan sai a diga flavour na vanilla a ciki sannan sai a markada su har sai sun yi kumfa sai a zuba a roba sannan a sanya shi a gidan sanyi (fridge) ya yi kankara._


_HADIN CHOCOLATE_:🍧
_A zuba madara da sukarin yin *cake* a na'urar markade ta gida (blender). Sannan a dauko cokali daya na 'pure cocoa' a zuba sannan a zuba *flavour* na kwakwa._

_Sannan sai a markada har sai ya yi kumfa sannan a zuba a roba. A dauko *chocolate* na maltisers a jefa a cikin hadin sannan a saka a gidan sanyi (fridge) ya yi kankara._


_Bayan haka za a iya dauko hadin *Vanilla* da wannan na *Chocolate* a hada sai a sha._

Comments

Popular posts from this blog

SAMOSA

SNACKS