FANKE
Abin Bukata filawa kofi 2 kofi 1 1/2 na ruwan dumi ckb 1 na yis 1/2 na sikari kc 1 na gishiri vanilla don dandano albasa kankararriya yadda za ayi a zuba yis cikin ruwan dumi don ya narke sai a zuba akan filawa tare da sikari, gishiri da vanilla a kwaba su baki daya yayi dan tauri a sami wuri me dumi a ajiye don ya tashi a sami kamar awa daya. a dora mai a wuta idan yayi zafi sai kisa hannunki ki dinga yankowa kina sawa a cikin man. idan ya soyu zaki ga ya zama ruwan kasa. za a iya ci da shayi ko kunu ko lemo. kada amanta kwabin kada ya zama ruwa-ruwa ko yayi tauri. aci dadi lafiya
Comments