Posts

Showing posts from June, 2015

romo

Image

shredded beef

Shredded beef ingredients: Nama ( tsoka Mara kitse),albasa,karas,green beans,attaruhu,citta tafarnuwa, Mai,corn flour, Magi,soy sauce, spice( oregano, black pepper, kwoi mixed spice,cumin, curry,cinnamon). Zaki samu naman ki ki yanka shi sirara dogaye akan chopping board,ki yanka karas dinki shima dogoye sirara ki yanka grean beans dinki dogaye,ki yanka albasa a tsatstsaye,ki jajjaga attaruhu,citta da tafarnuwa,. Method, ki samu kwano ki zuba yankakkun naman ki sai ki zuba duka spice din da soy sauce, magi,citta da tafarnuwa, attaruhu, da Dan gishiri idan kina bukata,ki jujjuya ki saka a fridge ya tsimu a kalla kamar na 30mins zuwa sama. Sai ki samu tukunyar ki ki zuba mai cokali 2 ki Dora a wuta ki zuba ragowar attaruhu da citta da tafarnuwar ki ki Dan soya,sai ki dauko naman ki ki juye a ciki ki jujjuya ki rufe ya rufu ruf(hikimar anan itace ruwan jikin naman ne zai tsatstsafo ya hadu da Dan mai din da kika zuba hakan zai saka naman yayi zaki tare da saurin dahuwa) sai ki na bude wa ...

MIYAN KUBEWA

Okro soup. Ingredients: kubewa, attaruhu,albasa,Manja,Ugu leaf( ganyen ugu), Ganda, stock fish,nama, Ghana pepper, dawadawa( iru)..METHOD,, zaki yayyanka kubewa ki daka ta tare da kanwar ungurnu kadan( don ya kara mata yauki) sai ki jajjaga attaruhu da albasa suyi laushi, ki daka Ghana pepper, ki daka dawa dawa( daddawar yarabawa ce suna kiranta IRU) ki yayyanka gandarki ki saka mata panadol idan ba mai laushi CE ba ki Dora ta a wuta har ta dahu,ki tafasa namanki da maggi da albasa,ki jika stock fish da ruwan zaki ki wanke, ki wanke ganyen ugun ki tas duk ki ajiye su.. Sai ki samu tukunyar miya ki Dora a wuta, ki zuba manja enof, idan ya fara soyuwa sai ki zuba dakakkiyar dawa dawa kinki ki barsu su soyo sai ki kawo jajjagaggen attaruhunki da albasa ki zuba ki juya idan suka dan soyu,sai ki zuba ruwan namanki da stockfish da gandarki,ki zuba maggi daidai ki rufe,idan ya tafasa sai ki dauko dakakkiyar kubewarki ki zuba ki juya ki rufe,idan kubewa ta kusa yi sai ki kawo ganyen ugu ki zub...

CHINESE RICE

Chinese Rice ingredients Shinkafa ( basmati ko tamu normal ma),tattasai,lawashi, karas, sweet corn( masarar gwangwani),Mai, citta da garlic, gishiri.. Note( chinese rice dai asali da basmati ake yinta,amma ni nayi da duka biyun kuma ya bani abinda nake nema,don haka tunda mafi akasari da normal shinkafa ake amfani bayanin yadda akeyi da ita zanyi.) Zaki wanke shinkafar ki da lemon tsami da gishiri yin haka yana sa ta kare haske, sai ki daurayeta sosai ki ajiye a kwalanda ta sha, sai ki samu lawashinki da tattasai dinki ki yanka cube, ki ajiye a gefe ki dau karas dinki kiyi grating dinsa kanana,ki jajjaga cittar ki da tafarnuwa a hade. Zaki zuba mai kadan a tukunya ki soya sai ki zuba shinkafar ki ki soyata sama sama ba suyar da zai canja mata kala ba( saboda gudun cabewa),sai ki Debi tafasasahen ruwa ki kwara akai daidai yadda zai dafa miki shinkafar amma ba lugub ba, idan ta danyi garaz garaz sai ki juye a kwalanda ki tace ta ki wanke domin cire starch din.ki mayar da ita wuta ki saka...

BEEF SOUP

BEEF SOUP (GHANA STYLE) INGREDIENTS: 1.Meat 2.Oil 3.Black pepper/Masoro dakakke 4.Salt, maggi, curry, 5.Garlic,onion,tomato, tomato paste 6.Citta 7.Carrots, potato PROCEDURE: Ki sami nama ki wanke shi, bayan kin yanka shi 'yan madaidaita, sai ki zuba a wani bowl, daga nan sai ki zuba masoro da citta, gishiri,maggi, curry da sauran kayan kamshi yadda zai ji, sai nikakken tafarnuwarki, sannan ki zuba yankakken albasa mai yawa. Sai ki juya su hade sosai. Daga nan sai ki sami tukunya ko frying pan mai dan zurfi ki zuba mai kamar ludayi daya, ki barshi ya dau zafi sai ki juye wannan naman duka. Ki barshi ya dan soyu kamar na minti 1 ko 2, sannan sai ki rufe. Ki sami wani karamin bowl, ki jajjaga tomato daya ko biyu , sannan ki sami tumatirin gwangwani cokali biyu babba ki zuba, sai ki dauko carrots da kika yanka su da fadi shi ma ki zuba a ciki ki jujjuya, sai ki juye a cikin naman nan da ke wuta ki jujjuya sosai. Daga nan sai ki zuba ruwa kamar kofi daya, ki barshi har sai naman ya kus...

roti chapatti

Roti/chapatti : zaki sama chapatti flour or normal flour!! Salt Warm water not hot

TANDURI CHICKEN

TANDURI CHICKEN Dafarko sai ku samu kazarku mai kyau ku wanketa tas a cire kayan ciki sannan sai ku barta ta tsane sannan sai ku samu man gyada ku shafe mata a jikinta sai ku sami kayan kanshi citta mai yatsu da citta mai kwaya da kuma masoro banda Kanunfari yanasa girki yai duhu sai ku sami kin ba duk dai ku hada ku dake idan suka daku sai ku bare tafarnuwa ku zuba in kuna so sai ku daka idan suka daku sai ku kwashe sannan sai ku zuba a wani dan kwano sai ku zuba ruwa kadan sannan ku zuba magi da curry da spcies na chicken sannan sai ku dan diga mai kadan a ciki sai ku juya sannan sai ku dauku rinka shafawa a jikin kazar nan cikinta da waje ya shafu sosai sai ku barta ta tsumu zuwa kamar awa daya sannan sai ku nemo farantin gashi ku dan shafa masa mai ko butter sai ku dora kazar nan akai kusa a oven ku barta taita Gasuwa amma wutar ku saka ta tsaka tsaki idan ta kusa gasuwa sai ku dan kara karfin wutar idan ta gasu sai ku sauke. Aci dadi lafiya Daga Batool

SNACKS

SAVOURY SNACKS: CONTENT: potato balls Yam balls Meat balls Flour balls Plantain balls Chicken balls Rice balls Indian balls Spring rolls Fish rolls Meat rolls Cabbage rolls Sausage rolls Casse role POTATO BALLS: kayan hadi: Dankali10 Nikakken nama Albasa 1 Attarugu 2 Kwai 2 Tafarnuwa Curry Maggi Gishiri Yadda ake yi: A tafasa dankali a bubbuga shi yayi laushi tubus. Sai a yanka albasa da attarugu a ciki. A zuba nikakken nama da maggi da gishiri da curry da tafarnuwa (idan ana bukatarta) a cakuda a hankali sai a dundunkula kamar kwallo (dai-dai girman da ake bukata.) A fasa kwai a kada, sai a rika tsoma cure-curen dankalin a ciki sannan a soya a ruwan mai. YAM BALLS: Kayan yadi: Doya 1 Nikakken nama Kwai 4 Albasa 4 Attarugu 4 Mai Maggi Gishiri Curry Yadda ake yi : A dafa doya sannan a bubbuga ta tayi laushi sai a hada ta da nikakken nama, a yanka albasa da attarugu, a zuba maggi, curry da gishiri. A motsa sosai sannan a rika curawa kamar kwallo, sai a tsoma a cikin ruwan kwai sannan a s...

ICE CREAM

KIRKIR Wani ice cream ne da larabawa kewa mazajen su, da farko zaki sami kwakwa ki goge bakin nan na bayan ta ki gurza ta jiki grater inda yake da kananan huji yadda zatayi siri-siri. Sai ki sa tukunya ki zuba ruwa kisa kwakwar ruwan yazama ya hau kan kwakwar maana ya rufe ta amma ba kindim ba sai kisa sugar. Yana tafasa sai ki kawo madarar gari ki zuba yadda zataji sosai sai ki juya ya hade ki barshi yayi kamar 3mins ki sauke ya huce sai kisa flavour na coconut. Kisa a fridge yayi ice sai aba mai house

Girki babban makamin diya mace na zaman aure

Eggs Carrot Peas  Corn  Onions  Garlic  Chili/attaruhu 1- Zaki samu basmati or long grain(rice irin tamu ta gida) ki dafata amma half done ba lugub ba kamar ni veges din wanda nake usn already adafe suke haka suke zuwa amma ke in danye ne naki zaki iya dafasu tare da rice din bayan kin yayyanka su. 2-Bayan rice tayi half done sai ki taceta kisa a gefe make sure ta tsane tsab. 3-Sai kisa pan a wuta da dan oil ki fasa eggs dinnan ki soya ki dagargaza shi sai kisa a bowl a gefe. 4-Kisaka oil a tukunya ni da olive oil nake amma zaki iyayi dako wanne irin oil din yayi zafi sai ki kawo albasar ki zuba kita juyawa sai tayi golden brown sai ki kawo rice+veges+attarihu ki zuba kita juyawa ki kawo egg dinnan da kika soya ki zuba ki saka duk seasoning din da kike so sai ki mayar da wuta low heat ki zuba hot water kadan wanda zai karasa dahuwar rice din sai ki kawo foil ki rufe ki dora marfin tukunya.wannan shine authentic method din Chinese sukeyi