TANDURI CHICKEN
TANDURI CHICKEN Dafarko sai ku samu kazarku mai kyau ku wanketa tas a cire kayan ciki sannan sai ku barta ta tsane sannan sai ku samu man gyada ku shafe mata a jikinta sai ku sami kayan kanshi citta mai yatsu da citta mai kwaya da kuma masoro banda Kanunfari yanasa girki yai duhu sai ku sami kin ba duk dai ku hada ku dake idan suka daku sai ku bare tafarnuwa ku zuba in kuna so sai ku daka idan suka daku sai ku kwashe sannan sai ku zuba a wani dan kwano sai ku zuba ruwa kadan sannan ku zuba magi da curry da spcies na chicken sannan sai ku dan diga mai kadan a ciki sai ku juya sannan sai ku dauku rinka shafawa a jikin kazar nan cikinta da waje ya shafu sosai sai ku barta ta tsumu zuwa kamar awa daya sannan sai ku nemo farantin gashi ku dan shafa masa mai ko butter sai ku dora kazar nan akai kusa a oven ku barta taita Gasuwa amma wutar ku saka ta tsaka tsaki idan ta kusa gasuwa sai ku dan kara karfin wutar idan ta gasu sai ku sauke. Aci dadi lafiya Daga Batool
Comments