shredded beef
Shredded beef ingredients: Nama ( tsoka Mara kitse),albasa,karas,green beans,attaruhu,citta tafarnuwa, Mai,corn flour, Magi,soy sauce, spice( oregano, black pepper, kwoi mixed spice,cumin, curry,cinnamon). Zaki samu naman ki ki yanka shi sirara dogaye akan chopping board,ki yanka karas dinki shima dogoye sirara ki yanka grean beans dinki dogaye,ki yanka albasa a tsatstsaye,ki jajjaga attaruhu,citta da tafarnuwa,. Method, ki samu kwano ki zuba yankakkun naman ki sai ki zuba duka spice din da soy sauce, magi,citta da tafarnuwa, attaruhu, da Dan gishiri idan kina bukata,ki jujjuya ki saka a fridge ya tsimu a kalla kamar na 30mins zuwa sama. Sai ki samu tukunyar ki ki zuba mai cokali 2 ki Dora a wuta ki zuba ragowar attaruhu da citta da tafarnuwar ki ki Dan soya,sai ki dauko naman ki ki juye a ciki ki jujjuya ki rufe ya rufu ruf(hikimar anan itace ruwan jikin naman ne zai tsatstsafo ya hadu da Dan mai din da kika zuba hakan zai saka naman yayi zaki tare da saurin dahuwa) sai ki na bude wa kina juyawa( idan kika barshi zai kama cz Mai din kadan ne) idan kikaga ya hada jikin sa sai ki debo ruwan daidai aukin da kike so miyar tayi sai ki zuba ki debo su karas dinki,green beans da albasa ki zuba ji juya( note kada yawan ruwan ya wucen yawan naman fa)ki Dan Dana idan kina da bukata ki kara magi ki Dada ki rufe,can ki bude ki juya ki taba kiji naman ya dahu su karas sun dahu, ga ruwa kuma tsululu ko a ciki ?yawwa sai ki samu kara min kwano ki debi corn flour ki zuba a ciki ki dama ta da ruwa kina zubawa a miyar kina juya miyar har zuwa kaurin da kike so tayi( idan kika cika corn flour bayan ta sha iska zata yi kauri kitif ki kula ana so tayi nan romo mai Dan kauri ne) sai ki bashi minti 2 sai ki sauke.( ki Sani idan bayan kin zuba ruwa kinga alamar akwai saura dayawa naman ya nuna toh kada ki zuba su karas dinki ki bari sai ya kusa yi,idan ba haka ba zasu dafe)..
Comments