Posts

Showing posts from February, 2015

romo

ROMON KAYAN CIKI _ ******___******___ Kayan ciki Kayan miya Kayan kamshi Tumatur Maggi,Gishiri Tafarnuwa Ganyen effirin Mai Zaki wanke kayan cikin ya wanku sosai da tumbi da hanji ki bubbude cikinsu ki wanke sosai kisa viniga ko lemon tsami ki wanke ki yanka su dai dai yadda ze miki,sai ki dora a wuta ki zuba magi da gishiri da dakakkiyar tafarnuwa ki yanka albasa ki barshi ya dahu,idan ya dahu sai ki kawo markaden kayan miya ki zuba amma kar yayi yawan da zatayi kauri. idan me gida yana bukatar yaji sai ki daka barkono ki kara ko attaruhu ki yanka albasa kanana ki zuba kayan kamshi tare da ganyen da kika yanka kanana kika wanke,amma ba dole sai kin sakashiba,ki saka mai ki barshi har yayi laushi,

ROMO

HAUSA DISHES

HAUSA DISHES. CONTENT: Dambun acha Alkubus Sinasir Gurasa Fankasu Waina/masa Burabusko DAMBUN ACHA kayan hadi: Acha kofi 2 Karas2 Kabeji 1/6 Albasa 1 Attarugu 2 Mai cokali 2 Alayyahu 1/2 kofi Maggi Gishiri Yadda ake yi : A wanke a rege acha, a yanka kabeji, karas, albasa, attaragu, da alayyahu a cakuda da achar a zuba mai, maggi da gishiri, a kara cakudawa sannan a zuba a madanbaci a turara kamar minti ashirin ko lokacin da komi ya dahu. ALKUBUS: Kayan hadi: Alkami kofi 2 Yeast cokali 1 Kanwa 1/2 cokali Gishiri 1/6 cokali Yadda ake yi: A kwaba alkama da ruwa da yeast a rufe a barta ta tashi, bayan awa biyar sai a zuba mata gishiri da ruwan kanwa yadda zata kashe tsamin. A kara cakudawa, idan yayi kauri dayawa a kara zuba ruwa kadan. A zuba a leda ko a gwangwani a turara kamar minti goma, za a ga ya tashi ya kumbura huf -hud kamar biredi. Ana cinsa da miyar ganye ko kuma kowace irin miya. SINASIR kayan hadi: Danyar shinkafa kofi biyu Yeast 1/2 cokali Gishiri 1/6 cokali Kanwa 1.2 cokali ...

PIMPLES

PIMPLES Pimples are small lesions or inflammations on the skin, mostly on the face. They are caused when sebaceous (oil) glands which get infected with bacteria and swell with pus. Now this is what you need most: 1. Don't touch or pop your pimple. It will open it up and cause more infections. 2. Wash your hands before you touch your face. You hands may spread the bacteria to your face. 3. Wash your face thoroughly and gently with medicated soap and warm water. 4. Don't wipe your face. Pat with a soft towel. Wiping spreads bacteria. 5. Change and wash your pillow case and bed sheets frequently 6. Use a mosturiser on your face. 7. Apply ice cubes on your face. This is anti-inflammatory. 8. Honey can also be applied to your face and left for about 20 minutes. 9. Apply lemon juice on your face. Do this at bedtime. 10. Antibacterial topical creams are also recommended.

BEANS

BEANS AND GREEN PEPPER CHICKEN Kayan hadi:- •Tsokar kaza •Mai •Koran tattasai •Tafarnuwa •Koran attaruhu •Danyar citta •Albasa mai lawashi •Dark soy souce •Maggi/Gishiri •Wake YADDA AKE HADAWA yanka tsokar kaza kanana kanana,dafa wake har sai yayi laushi,zuba mai a kasko soya citta da tafarnuwa soya sama sama, zuba kaza ci gaba da juyawa a hankali.zuba ruwa dai dai yadda zai dafa kazar zuba wannan dafaffen waken da Koran tattasai,attaruhu,albasa,maggi da dai sauran kayan kamshi,ci gaba da juyawa ,idan kazar ta dahu sauke.za’a iya cin wannan miyar haka ko kuma da farar shinkafa ko buredi.

KAFTA

KAFTA _ ___ Tsokar kaxa Albasa Attaruhu Lawashin albasa Koran tattasai Maggi&Gishiri Curry Mai,ko butter Tafarnuwa YADDA AKEYI Dama kin gyara kaxar ki kin cire duk kashin dake jikinta sai ki markadata yadda zata yi laushi sai ki aje ta ki yanka koren wake koran tattasai lawashin albasa ki wanke ki jajjaga attaruhu da albasa ki juye su duka a cikin naman ki juya sosai ki fasa kwai ki kadashi ki zuba tare da magi gishiri tafarnuwa da curry ki jujjuya su sai ki kawo leda kamar girman ta bread ki juye a ciki ki dafa kamar alala amma fa ya dahu sosai. idan ya dahu sai ki sauke ki yayyanka shi kamar haka ki shafa masa butter ki gasashi a oven ko ki soya shikenan.

QOSAN KAZA

♥♥ QOSAN KÁZÁ ♥♥ #Kwadayi mode activated!!! #Ki samu tsokar kaza zalla,banda qashi. #ki yayyanka qanana ki zuba a blender. #ki zuba magu,curry,tafarnuwa and other spices of ur choice. #ki yi blending dinshi duka. #ki soya mai kamar zakiyi qosai,in yayi zafi sai kiyi ta sa kawa kamar kina soya qosai.... Mhmmmm,zaki bani labarin dadinsa!!

MACARONI MAI ROMO

MACARONI ME ROMO _ ______________ Macaroni Fulawa Nama Kwai Albasa Attaruhu Mai Maggi Gishiri Curry YADDA AKE Zaki dafa macaroni da ruwa ki taceta ki aje,ki dora namanki a wuta na kaza ko na sa ki tafasashi da magi da albasa da gishiri ki dan zuba markadan kayan miya kadan akai tare da mai su yi ta dahuwa. idan sun dahu ruwan ciki ya zama romo sai ki dama yar fulawarki ki zuba aciki da magi gishiri da curry, sai ki dafa kwai ki a guda gudansa ki saka a ciki ki juye shima macaronin a ciki ki barshi 5mins sai ki sauke da ruwansa akeci ga kuma kwai ana ci da safe haka.

ADO DA KWALLIYA

Jama'a barkanmu da dare. Acikin filinmu na ado da kwalliya yau zamu fadi yadda ake gyara fuska da yadda akewa fuska kwalliya,saboda fuska tanada makuqar muhimmanci da jan hankali acikin kwalliya. Zamu fara da yadda ake gyara fuska kafin ayi mata kwalliya,yadda fuska zatai taushi da haske sannan bazatai kurajeba ,tayadda bazamu kashe kudinmu wajen siyan man qara hasken fuska ba wato(lightening cream). masu kurajen fuska zasu samu lemon tsami a matseshi a hada ruwansa da ruwan veniger wato(ma'u khal)saiki shafa da auduga a hankali kibarshi yai minti 20(akiyaye karya shiga ido). Ana kwaba lalle da sai asa dan ruwan ma'u khal acikinsa sai a shafa a fuska a barshi yai minti 10,yanasa taushi da hasken fata,fatarki zatayi danja maiban sha'awa. 'bawon Gwanda yana maganin kurajen fuska kuma fuska zatai santsi za a gogashi a fuska sai a barta tayi minti 30 kafin a wanke. 'Bawon kankana da tumatur yana gyara fuska shima za a gogashi abarshi y...

About Aysher Bappah Kani

Placeholder for About Me page of Aysher Bappah Kani