HAUSA DISHES

HAUSA DISHES. CONTENT: Dambun acha Alkubus Sinasir Gurasa Fankasu Waina/masa Burabusko DAMBUN ACHA kayan hadi: Acha kofi 2 Karas2 Kabeji 1/6 Albasa 1 Attarugu 2 Mai cokali 2 Alayyahu 1/2 kofi Maggi Gishiri Yadda ake yi : A wanke a rege acha, a yanka kabeji, karas, albasa, attaragu, da alayyahu a cakuda da achar a zuba mai, maggi da gishiri, a kara cakudawa sannan a zuba a madanbaci a turara kamar minti ashirin ko lokacin da komi ya dahu. ALKUBUS: Kayan hadi: Alkami kofi 2 Yeast cokali 1 Kanwa 1/2 cokali Gishiri 1/6 cokali Yadda ake yi: A kwaba alkama da ruwa da yeast a rufe a barta ta tashi, bayan awa biyar sai a zuba mata gishiri da ruwan kanwa yadda zata kashe tsamin. A kara cakudawa, idan yayi kauri dayawa a kara zuba ruwa kadan. A zuba a leda ko a gwangwani a turara kamar minti goma, za a ga ya tashi ya kumbura huf -hud kamar biredi. Ana cinsa da miyar ganye ko kuma kowace irin miya. SINASIR kayan hadi: Danyar shinkafa kofi biyu Yeast 1/2 cokali Gishiri 1/6 cokali Kanwa 1.2 cokali Mai cokali 1 Sikari cokali 1 Yadda ake yi: A jika shinkafa da ruwa ta kwana sai a wanke shinkafar a nika, a zuba yeast da nono a juya se a rufe ta sake kwana ko a kalla awa 12 zuwa sama. Da safe a motsa a zuba gishiri da ruwan kanwa yadda zai isa. A shafa mai a kwanon tuya (fraying pan) idan yayi zafi sai a zuba kullin ludayi biyu a rufe, kamar minti 1 ko biyu ya dahu sai a sauke a sake goga mai a zuba wani. Ana ci da miyar ganye ko miyar agushi. GURASA: kayan hadi: Filawa kofi 2 Hoda 1/2 cokali Gishirin kadan Mai cokali 1 Yadda ake yi: A kwaba filawa, hoda, gishiri, mai kadan da ruwa. A rufe bayan minti talatin a mirza ta tayi fadi sosai sai a soya a ruwan mai. Ana ci da miya ko sif. FANKASU kayan hadi: Alkama kofi 2 Yeast 1/2 cokali Kanwa 1/2 cokali Gishiri kadan Mai Yadda ake yi: A kwaba alkama da ruwa da yeast. A rufe a barta ta kumbura har awa biyar ko sama da haka. Idan ta tashi sosai sai a zuba gishiri da ruwan kanwa, kwabin ya danyi ruwa-ruwa amman yadda za a iya dauka a hannu a danyi fadi dashi a soya a ruwan mai. Ana ci da miyar agushi, ganye ko taushe. WAINA/MASA Kayan hadi: Shikafa kofi 2 Kanwa 1/2 cokali Yeast 1/2 cokali Gishiri 1/6 cokali Nono cokali 1 Sikari 1 Yadda ake yi : A jika danyar shinka da ruwa ta kwana daya ko biyu sai a markada a zuba nono da yeast ta sake kwana. Da safe a zuba mata gishiri da ruwan kanwa yadda zai isa da sikari. Sai a zuba mai kadan a tanda a soya. Ana cin waina da miya ko sugar ko kuli.

Comments

Popular posts from this blog

SAMOSA

SNACKS