Posts

Showing posts from March, 2017
Image
SUYAR DANKALIN TURAWA  DANKALI KARAS KOREN TATTASAI QWAI MAGGI CURRY THYME  Zaki samu dankalin ki ki fereye shi ki yankashi shafe din da ki keso, ki wanke shi ki tsane da colander, sannan zaki dora man ki  a wuta yayi zafi, saiki dauko dankalin ki ki saka masa gishiri ki gauraya, ki zuba amanki ki barshi ya soyu sosai kina juyawa saiki kwashe,      Zaki yanka Karas dinki da koren tattasai yadda ki keso bayan kin kankare karas din kin wanke koren tattasai dinki, saiki mai kadan a frynpan kidan soya su sama sama, saiki kada qwan ki  a kwano kisa masa maggi thyme curry, ki kawo dankalin ki da kika soya ki juye akan qwan ki, ki kawo karas da tattasan kijuye kiy mixn din su, saiki qara mai a pan din ki yayi zafi ki juye hadin dankalin ki, ki na juya shi har sai ya soyu, aci dadi lfy.
Image
YADDA ZAKIYI DOYA DA QWAI MAI KYAU DA DADI    Idan kika tafasa doyar ki da gishiri zaki sauqeta ta huce, sanna zaki yanka ta yadda kike so, sai ki fasa qwanki a kwano ko roba mai dan fadi daidai yadda ki keso, zaki kawo maggi da curry Kayan qamshin da ki keso ki barbada a saman qwan, karki kada qwan saboda in kin kada bazai kama jikin doyar ba, sai ki dora man ki a frynpan yayi zafi, sannan sai kina tsoma doyar da daya daya a ruwan qwan kina sakawa a man da kika dora, kina iya yanka albasa a ruwan qwan, da zaran kinga ta soyu sai ki juya bayan haka zakiyi tayi kina kwashewa har ki gama.
Image
DASHISHI/BISKIN ALKAMA    Zaki samu alkamar ki ki cire mata datti agyara ta, sai abarza ta kamar zakiyi zakiyi biski, in an barza zaki samu gittere na turara abinci kijuyeta , saiki dora a tukunya kisa ruwa a tunkunyan kibarshi ya tafasa ya turara garin alkamar sosai, sai ta fara qamshi, sannan ki sauqe ki rage ruwan tukunyan kibar kadan, saiki kawo mangyada kamar ludayi daya kizuba a ruwan tukunyan, ki kawo garin da kika turara ki juye ki tuqa shi, sai ki rage wuta ki barshi ya nuna kafin ki kwashe, zaa iya cin dashishi da miyar ja, miyar romo, DSS Ayyush #
Image
MASA Shinkafa fara ta tuwo Yeast Sugar Albasa Kanwa Mai   Da farko zaki samu shinkafar ki kamar Rabin mudu saiki raba ta gida hudu kijiqa kashi uku saiki tafasa kashi dayan, idan kin wanketa saiki hada ta da jiqaqqiyar a markada sai ki saka mata yeast kirufe ta, idan lokacin sanyi ne kina iya qara mata nono don tayi saurin tashi tayi tsami, daga tayi tsami zaki dauko ta qullun ki ki dama shi kiyanka albasa kisa sugar da kanwa kadan, sannan saiki dora abin suyanki tayi zafi kisa mai kowane gida, sai kina debo qullun kina zubawa yadan fi Rabin ramin suyan naki, a hankali kisa wuta kadan kadan kibar ta ta nuna sai ki juya bayan haka zakiyi tayi har ki gama, ana iya cin masa  da miyan taushe, miyan ganye, miyan egusi, DSS. #Ayyush
Image
CAKE A TOASTER    Zaki kwaba cake normal yadda ake kwabawa saidai kar yayi na gashin oven tauri   Sannnan zaki kunna toaster ko sandwichmaker dinki yayi zafi sannan zaki samo brush kina dangwala butter a cikin ramukan toaster din duk ki shafa,    Bayan kin gama zaki dauko kwabin cake dinki kina zuzzuba wa kilura karki cika da yawa saiki rufe toaster din zuwa minti 3ko4 idan ta dau zafi saiki bude ki duba in yayi zaki cire in baiyi ba saiki juya daya side din ki sake rufewa har ya gasu.
Image
PANCAKE KAYAN HADI •flour kofi daya •Sugar cokali 2 •Baking powder babban 1 •Kwai daya •Madara peak daya (ko na gari ne zaki iya saka 2-3 table spoon ki dama da ruwa cikin gwangwanin madara karami) •Butter/oil •Gishiri kadan YAD Cikin kwano mai fadi a hada tankadadden flour, sugar, bakin powder da gishiri. Ki fasa kwai cikin madara da 1 table spoon of oil ki kada ki juye cikin flour sai ki dama shi Idan yayi ruwa sosai sai ki 'kara flour kadan, ana son kwabin yafi na wainar flour/kalallaba kauri kadan. ki saka 1 tbsp na butter/oil a frying pan in yayi zafi sai ki debe kwabin dai-dai misali ki zuba, ki yi fadi dashi kamar zaki soya kwai, idan side daya yayi sai ki juya dayan side din.