Posts

Showing posts from March 8, 2017
Image
CAKE A TOASTER    Zaki kwaba cake normal yadda ake kwabawa saidai kar yayi na gashin oven tauri   Sannnan zaki kunna toaster ko sandwichmaker dinki yayi zafi sannan zaki samo brush kina dangwala butter a cikin ramukan toaster din duk ki shafa,    Bayan kin gama zaki dauko kwabin cake dinki kina zuzzuba wa kilura karki cika da yawa saiki rufe toaster din zuwa minti 3ko4 idan ta dau zafi saiki bude ki duba in yayi zaki cire in baiyi ba saiki juya daya side din ki sake rufewa har ya gasu.
Image
PANCAKE KAYAN HADI •flour kofi daya •Sugar cokali 2 •Baking powder babban 1 •Kwai daya •Madara peak daya (ko na gari ne zaki iya saka 2-3 table spoon ki dama da ruwa cikin gwangwanin madara karami) •Butter/oil •Gishiri kadan YAD Cikin kwano mai fadi a hada tankadadden flour, sugar, bakin powder da gishiri. Ki fasa kwai cikin madara da 1 table spoon of oil ki kada ki juye cikin flour sai ki dama shi Idan yayi ruwa sosai sai ki 'kara flour kadan, ana son kwabin yafi na wainar flour/kalallaba kauri kadan. ki saka 1 tbsp na butter/oil a frying pan in yayi zafi sai ki debe kwabin dai-dai misali ki zuba, ki yi fadi dashi kamar zaki soya kwai, idan side daya yayi sai ki juya dayan side din.