MASA



Shinkafa fara ta tuwo

Yeast

Sugar

Albasa

Kanwa

Mai


  Da farko zaki samu shinkafar ki kamar Rabin mudu saiki raba ta gida hudu kijiqa kashi uku saiki tafasa kashi dayan, idan kin wanketa saiki hada ta da jiqaqqiyar a markada sai ki saka mata yeast kirufe ta, idan lokacin sanyi ne kina iya qara mata nono don tayi saurin tashi tayi tsami, daga tayi tsami zaki dauko ta qullun ki ki dama shi kiyanka albasa kisa sugar da kanwa kadan, sannan saiki dora abin suyanki tayi zafi kisa mai kowane gida, sai kina debo qullun kina zubawa yadan fi Rabin ramin suyan naki, a hankali kisa wuta kadan kadan kibar ta ta nuna sai ki juya bayan haka zakiyi tayi har ki gama, ana iya cin masa  da miyan taushe, miyan ganye, miyan egusi, DSS. #Ayyush

Comments

Ahmad said…
Godiya

Popular posts from this blog

SAMOSA

SNACKS