COCONUT RICE

coconut-tomato-rice.jpg Abin Bukata ruwan kwakwa kofi 5 shinkafa gwangwani 3 timatir manya 5 timatirin gwangwani 1 mai madaidaici kanunfari kc1 gishiri don dandano ganye bay kadan albasa attaruhu kadan tafarnuwa Yadda Za Ayi a dafa ruwan dumi a zubawa shinkafa kafin a dafa ta. a jajjaga attaruhu tare da tafarnuwa. asa mai a wuta idan ya soyu sai a zuba jajjagaggun kayan miya a kawo timatirin gwangwanin nan a zuba akai su soyu gaba daya idan sun soyu sai a zuba ruwan kwakwan nan akai tare da ganyen bay. daya tafaso sai a wanke shinkafa a zuba a rufe ta idan ana so a hada ta dankalin turawa a zuba mata gishiri daidai gwargwadon bukata. idan ta dahu za a iya cin ta da naman kaza soyayyaye ko kifi. wannan dafadukar wata nauin dafaduka ce da babbain ta da wanda aka sani shine ruwan kwakwa da aka sa. a wasu kashen afrikan ake yinta kamar cameroun kuma ana girka ta da nama amma wannan na bada zabi za a iya anfani da abin da ake bukata.kamar wanda basa cin nama zasu iya anfani da wannan hadin.

Comments

fatima bello bala said…
Allah biya.
hameeda abubakar said…
Yayi daidai
Ashraf said…
Mungode
maman suhaima said…
godiya ba adadi allah yasa d alkhairi ameen

Popular posts from this blog

SAMOSA

SNACKS