vegetable sauce

VEGETABLE SAUCE
INGREDIENTS:
1.Fish,Oil
2.Lawashi, Tomatoes,
3.Alayyaho/Ugwu ,green beans
4.Maggi, gishiri
5.Kanunfari, citta, curry, thyme, onga da sauran kayan
kamshi.
PROCEDURE:
Ki sami kifi mai kyau ki gyara ki wanke, ki zuba a
tukunya, ki wanke tukunya ki sa a wuta, yana fara zafi
sai ki dauko kifi ko nama ko kaza ki sa a ciki, sai ki sa
maggi amma kada ki farfasa ki sashi a haka, sai ki
dauko isashen lawashin da kika yanka, ki juye a ciki, ki
dauko carrots da kika kankare kika yanka kanana ki
juye a ciki, ki sa green beans daga nan sai ki dauko
ruwa wanda zai shanye kan kifin ko kazan ki zuba a
ciki. Ki zuba mangyada dan dai-dai, sai ki rufe ki barshi
ya tauso.
Daga nan sai ki jajjagaga tumatir ko ki yanka, idan
kuma kina son su tarugu duk sai ki sa, ki sa gishiri,
curry, thyme, citta, onga da sauran kayan kamshin da
na lissafo sai ki rufe ya cigaba da dahuwa, sai ki dauko
yankakken alayyahon ki zuba a sama, ki rufe, bayan
kamar 5mnt sai ki dan jujjuya, a hankali zaki yi saboda
kada kifinki ya farfashe, sannan ki dandana maggi da
gishiri idan bai ji ba ki kara.
Note: Vegetable sauce ko soup zaki iya sa masa duk
abinda kike so dayaa kkunshi vegetables, ba wai ddole
sai abinda na lissafo ba.
Vegetable soup ba a ya so dahu dayawa, don duk zasu
narke ne. Don haka sai ki kula. Ana cinsa zalla, ana
cinsa da shinkafa, ko doya ko dankali. Sannan yara
suna enjoying sauce dinnan, haka ma marasa lafiya.

Comments

Kamisu ismaila said…
Slm inawa wannan filin fatan alkairi
Maryam m.sani said…
Idan anwanke kifin ba ayankasa kanana

Popular posts from this blog

SAMOSA

SNACKS