Posts
Showing posts from September 1, 2015
MASAR DANKALI
- Get link
- X
- Other Apps
MASAR DANKALI *dankali *kwai *attaruhu *maggi *albasa *gishiri *curry Ki feraye dankali ki dafa dankali ya dahu sosai yayi luguf,sannan ki dauko wata yar roba me zurfi ki zuba dankan. Ki debo kwai masu dan yawa ki fasa akan dankalin sannan ki dauko ludayi ki dama ya damu sosai ya zama sun hada jikinsu. Sai ki dauko attaru da albasa ki jajjaga sai ki zuba akan wannan dankalin da kika dama sai ki dauko maggi,gishiri,curry ki zuba akai sai ki kara damawa ya damu sosai. Sai ki dauko tanda ki dora akan wuta ki xubawa ko wane kusurwa mai aciki,sai ki dauko wannan kullun dankalin ki xuba acikin ko wace kusurwa ki barshi yadan yi mintuna saboda cikin masar ya dahu,sai ki juyata,in tadanyi mintuna sai ki kwashe.zakiga tai kyan gani sannan kuma tayi irin shape din masar shinkafa
dambun shinkapa
- Get link
- X
- Other Apps
DAMBUN SHINKAFA Shinkafa Karas Koren wake kabeji albasa,attaruhu maggi,gishiri hanta mangyada dafarko kisamu shinkafarki iya adadin dakike bukata, kikai a barzo miki. Kifidda garin tahanyar tankadewa kidauki tsakin kiwanke shi tas! Kizuba amadanbaci, kirufe ruf da leda sannan kidaura awuta kikawo murfi kirufe dan ba'aso tiririn yadinga fita. Kitabbatar kinxuba ruwa a kasan tukunyar daidai yadda baxai koneba. Kitafasa karas dinki sama sama. Ba lugub ba kiyayyankashi bayan kin kankare bayan. Shima koren wakenki kitafasashi, akwai wanda ake siyarwa bararre kuma busasshe todashi xaki amfani. Kabejin ma kiwankeshi tas kiyanka amma ba kanana chanba. Attaruhu da albasa kiyankasu suma yadda kike bukata. Anaso albasar tayi yawa. Hantarki kitafasa da isasshen maggi da dan gishiri, kiyanka gutsi-gutsi. Bayan tsakinki yayi laushi saiki sauke kizuba mai yakamashi, sannan kikawo kayan lambun nan kixuba, kicakudasu yadda xasu hade jikinsu da tsakin hakama attaruhu da albasarnan hadida yankakken h...
YADDA AKE DANBUN NAMAN KAZA
- Get link
- X
- Other Apps
Idan kika gyara kajinki tas! Saikicire masa fatar dake jiki gaba daya kiwanke yadda ya kamata Saiki zuba a tukunya amma kizuba ruwa kwatan kwacin yadda naman zai shanye, karki zuba dayawa, kidora kiyanka albasa, maggi, gishiri, curry, da kayan qamshi zabinki, saiki rufe kibarta tayi tafasa dakin bude kinga naman yayi laushi zaki sauke qasa saiki sa muciya kiyi ta faffasa naman idan baki cire fatar yana danye ba to yanzu saiki zare duk fatar da manyan qashi kiyta faffasawa zakiga naman yafito sanka-sanka saiki jajjaga taruhunki sosai, kijuye akai ki qara curry da kayan qamshin dakike so, ki gauraye ya hade nam an, saiki samu abun suya mai dan dama kizuba mai dayawa cux inkika masa qwauron mai kwata kwata bazaiyi kyau ba, sannan bazai laushi ba,saiki dauko namanki kijuye aciki kidora awuta kipara soyawa sannan kisa wuta kadan ahankali kina juyawa akai akai,idan ya soyu zakiga yayi ja sannan mai zaipara kumpa kuma zakiji qamshi saiki sauqe kijuye a colander ya huce saiki dan saka plate as...