MASAR DANKALI

MASAR DANKALI
*dankali
*kwai
*attaruhu
*maggi
*albasa
*gishiri
*curry
Ki feraye dankali ki dafa dankali ya dahu sosai yayi luguf,sannan ki dauko wata yar roba me zurfi ki zuba dankan. Ki debo kwai masu dan yawa ki fasa akan dankalin sannan ki dauko ludayi ki dama ya damu sosai ya zama sun hada jikinsu. Sai ki dauko attaru da albasa ki jajjaga sai ki zuba akan wannan dankalin da kika dama sai ki dauko maggi,gishiri,curry ki zuba akai sai ki kara damawa ya damu sosai. Sai ki dauko tanda ki dora akan wuta ki xubawa ko wane kusurwa mai aciki,sai ki dauko wannan kullun dankalin ki xuba acikin ko wace kusurwa ki barshi yadan yi mintuna saboda cikin masar ya dahu,sai ki juyata,in tadanyi mintuna sai ki kwashe.zakiga tai kyan gani sannan kuma tayi irin shape din masar shinkafa

Comments

khadijat said…
Thanks
Husnah Al-ameen said…
Yummy!! tanks a lot.
fiedausy said…
yum yum. mungode

Popular posts from this blog

SAMOSA

SNACKS