dambun shinkapa
DAMBUN SHINKAFA
Shinkafa
Karas
Koren wake
kabeji
albasa,attaruhu
maggi,gishiri
hanta
mangyada
dafarko kisamu shinkafarki iya adadin dakike bukata, kikai a barzo miki. Kifidda garin tahanyar tankadewa kidauki tsakin kiwanke shi tas! Kizuba amadanbaci, kirufe ruf da leda sannan kidaura awuta kikawo murfi kirufe dan ba'aso tiririn yadinga fita. Kitabbatar kinxuba ruwa a kasan tukunyar daidai yadda baxai koneba.
Kitafasa karas dinki sama sama. Ba lugub ba kiyayyankashi bayan kin kankare bayan. Shima koren wakenki kitafasashi, akwai wanda ake siyarwa bararre kuma busasshe todashi xaki amfani. Kabejin ma kiwankeshi tas kiyanka amma ba kanana chanba.
Attaruhu da albasa kiyankasu suma yadda kike bukata. Anaso albasar tayi yawa. Hantarki kitafasa da isasshen maggi da dan gishiri, kiyanka gutsi-gutsi. Bayan tsakinki yayi laushi saiki sauke kizuba mai yakamashi, sannan kikawo kayan lambun nan kixuba, kicakudasu yadda xasu hade jikinsu da tsakin hakama attaruhu da albasarnan hadida yankakken hantarnanan kihada kisake juyawa, sannan kidan daka maggi da gishiri kadan yadda baxaiyi yawaba kicakuda kimayar wuta.
Kibashi lokaci xakiji yana fidda kamshi sosai kitabbatar yayi kamshi kuma ya dahu sosai yadda akeso, ki sauke. Xa'a iya ci a haka, kokuma kiyi masa miyar kayan lambu
Comments