Jama'a barkanmu da dare. Acikin filinmu na ado da kwalliya yau zamu fadi yadda ake gyara fuska da yadda akewa fuska kwalliya,saboda fuska tanada makuqar muhimmanci da jan hankali acikin kwalliya. Zamu fara da yadda ake gyara fuska kafin ayi mata kwalliya,yadda fuska zatai taushi da haske sannan bazatai kurajeba ,tayadda bazamu kashe kudinmu wajen siyan man qara hasken fuska ba wato(lightening cream). masu kurajen fuska zasu samu lemon tsami a matseshi a hada ruwansa da ruwan veniger wato(ma'u khal)saiki shafa da auduga a hankali kibarshi yai minti 20(akiyaye karya shiga ido). Ana kwaba lalle da sai asa dan ruwan ma'u khal acikinsa sai a shafa a fuska a barshi yai minti 10,yanasa taushi da hasken fata,fatarki zatayi danja maiban sha'awa. 'bawon Gwanda yana maganin kurajen fuska kuma fuska zatai santsi za a gogashi a fuska sai a barta tayi minti 30 kafin a wanke. 'Bawon kankana da tumatur yana gyara fuska shima za a gogashi abarshi y...
Comments