SNACKS
SAVOURY SNACKS: CONTENT: potato balls Yam balls Meat balls Flour balls Plantain balls Chicken balls Rice balls Indian balls Spring rolls Fish rolls Meat rolls Cabbage rolls Sausage rolls Casse role POTATO BALLS: kayan hadi: Dankali10 Nikakken nama Albasa 1 Attarugu 2 Kwai 2 Tafarnuwa Curry Maggi Gishiri Yadda ake yi: A tafasa dankali a bubbuga shi yayi laushi tubus. Sai a yanka albasa da attarugu a ciki. A zuba nikakken nama da maggi da gishiri da curry da tafarnuwa (idan ana bukatarta) a cakuda a hankali sai a dundunkula kamar kwallo (dai-dai girman da ake bukata.) A fasa kwai a kada, sai a rika tsoma cure-curen dankalin a ciki sannan a soya a ruwan mai. YAM BALLS: Kayan yadi: Doya 1 Nikakken nama Kwai 4 Albasa 4 Attarugu 4 Mai Maggi Gishiri Curry Yadda ake yi : A dafa doya sannan a bubbuga ta tayi laushi sai a hada ta da nikakken nama, a yanka albasa da attarugu, a zuba maggi, curry da gishiri. A motsa sosai sannan a rika curawa kamar kwallo, sai a tsoma a cikin ruwan kwai sannan a s...
Comments