CHINESE RICE

Chinese Rice ingredients Shinkafa ( basmati ko tamu normal ma),tattasai,lawashi, karas, sweet corn( masarar gwangwani),Mai, citta da garlic, gishiri.. Note( chinese rice dai asali da basmati ake yinta,amma ni nayi da duka biyun kuma ya bani abinda nake nema,don haka tunda mafi akasari da normal shinkafa ake amfani bayanin yadda akeyi da ita zanyi.) Zaki wanke shinkafar ki da lemon tsami da gishiri yin haka yana sa ta kare haske, sai ki daurayeta sosai ki ajiye a kwalanda ta sha, sai ki samu lawashinki da tattasai dinki ki yanka cube, ki ajiye a gefe ki dau karas dinki kiyi grating dinsa kanana,ki jajjaga cittar ki da tafarnuwa a hade. Zaki zuba mai kadan a tukunya ki soya sai ki zuba shinkafar ki ki soyata sama sama ba suyar da zai canja mata kala ba( saboda gudun cabewa),sai ki Debi tafasasahen ruwa ki kwara akai daidai yadda zai dafa miki shinkafar amma ba lugub ba, idan ta danyi garaz garaz sai ki juye a kwalanda ki tace ta ki wanke domin cire starch din.ki mayar da ita wuta ki saka ruwan zafi kadan ta Dan karasa dahuwa kamar dahuwar hotel haka, sai ki juye a kwalanda ki ajiye ta sha.. Sai ki samu tukunyar ki ki zuba mai kadan tare da citta da tafarnuwa, da yankakken tattasai da lawashinki ki soya su sama sama sai ki debo shinkafar ki ki zuba akai ki cigaba da soyasu kina juyaga a hankali cz kada ta cabe, idan kika ga sun hada jikin su sai ki zuba karas dinki da kika goga a grater Dan dai yadda zaki na ganin sa daya daya a shinkafar ki ba dawa ba, ki bude gwangwanin masarar ki ki debo ki zuba shi shima daidai, sai ki bar bada gishiri kadan ki jujjuya su su Dan kara soyuwa komai ya yi daidai...zaki ga yayi wara wara tana kyalli(ki kula kada ki cika mai cokalin cin abinci daya ko biyu ya isa ya danganta da yawar shinkafar ki) Na basmati rice yafi saukin yi ga meson method din

Comments

NUWAIRA said…
dolene sai da masarar gwangwani baxa ayi da ta gidaba

Popular posts from this blog

SNACKS

SAMOSA