BEEF SOUP
BEEF SOUP (GHANA STYLE) INGREDIENTS: 1.Meat 2.Oil 3.Black pepper/Masoro dakakke 4.Salt, maggi, curry, 5.Garlic,onion,tomato, tomato paste 6.Citta 7.Carrots, potato PROCEDURE: Ki sami nama ki wanke shi, bayan kin yanka shi 'yan madaidaita, sai ki zuba a wani bowl, daga nan sai ki zuba masoro da citta, gishiri,maggi, curry da sauran kayan kamshi yadda zai ji, sai nikakken tafarnuwarki, sannan ki zuba yankakken albasa mai yawa. Sai ki juya su hade sosai. Daga nan sai ki sami tukunya ko frying pan mai dan zurfi ki zuba mai kamar ludayi daya, ki barshi ya dau zafi sai ki juye wannan naman duka. Ki barshi ya dan soyu kamar na minti 1 ko 2, sannan sai ki rufe. Ki sami wani karamin bowl, ki jajjaga tomato daya ko biyu , sannan ki sami tumatirin gwangwani cokali biyu babba ki zuba, sai ki dauko carrots da kika yanka su da fadi shi ma ki zuba a ciki ki jujjuya, sai ki juye a cikin naman nan da ke wuta ki jujjuya sosai. Daga nan sai ki zuba ruwa kamar kofi daya, ki barshi har sai naman ya kusa gama dahuwa sai ki zuba dankali, sannan ki sake jajjaga albasa mai yawa ki zuba. Sai ki sake zuba ruwa kofi daya ki barshi ya cigaba da dahuwa har sai sun yi luguf. Zaki iya dandana maggi Gishiri idan bai ji ba ki kara ki barshi su karasa dahuwa.
Comments